1 Samaʼila 14:41 - Littafi Mai Tsarki41 Sa'an nan Saul ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa ba ka amsa mini ba a wannan rana? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Jonatan, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka nuna mana.” Sai amsa ta nuna Jonatan da Saul ne, jama'a kuwa suka kuɓuta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202041 Sa’an nan Shawulu ya yi addu’a ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, “Me ya sa ba ka amsa mini addu’ata a yau ba? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Yonatan, ka nuna mana ta wurin Urim, amma idan laifin mutanen ne ka amsa ta wurin Tummim.” Ba a sami mutane da laifi ba, amma ƙuri’a ta fāɗa a kan Yonatan da Shawulu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |