Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 14:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Sai wani daga cikin jama'a ya ce, “Ai, mahaifinka ya yi wa mutane barazana da rantsuwa cewa, ‘La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana.’ ” Mutane kuwa suka tafke.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Sai wani soja ya gaya masa cewa, “Mahaifinka ya sa kowa ya yi rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana!’ Shi ya sa duk sojojin ba su da ƙarfi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 14:28
4 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Saul ya ce wa Jonatan, “Ka faɗa mini abin da ka yi!” Jonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana 'yar zuma ne da na lakata da kan sandan da yake hannuna, ga ni, a shirye nake in mutu.”


A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.


Amma Jonatan bai ji barazanar da mahaifinsa ya yi wa jama'a ba, sai ya lakaci saƙar zuma da kan sandansa ya sa a hannu ya kai baka, sa'an nan idanunsa suka buɗe.


Jonatan kuwa ya ce, “Lalle mahaifina ya wahalar da jama'a! Dubi yadda na wartsake sa'ad da na ɗanɗana 'yar zuman nan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ