1 Samaʼila 13:19 - Littafi Mai Tsarki19 A wannan lokaci ba maƙeri a ƙasar Isra'ila duka, domin Filistiyawa sun hana Ibraniyawa su ƙera wa kansu takuba ko māsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.