Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 13:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Sai Sama'ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Saul ya amsa ya ce, “Don na ga mutane suna watsewa, suna barina, kai kuma ba ka zo daidai lokacin ba, ga kuma Filistiyawa sun tattaru a Mikmash.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Shawulu ya ce, “Sa’ad da na ga mutane suna watsewa, kai kuwa ba ka zo cikin lokaci ba, ga Filistiyawa kuma suna taruwa a Mikmash,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 13:11
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ƙungiyar sojojin Filistiyawa ta fita zuwa mashigin Mikmash.


Sai Saul da ɗansa, Jonatan, da mutanen da suke tare da su suka zauna a Geba ta Biliyaminu. Filistiyawa kuwa suka kafa sansaninsu a Mikmash.


Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000), da mahayan dawakai dubu shida (6,000), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen.


Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga Isra'ila, dubu biyu (2,000) su zauna tare da shi a Mikmash da ƙasar tuddai ta Betel, dubu ɗaya (1,000) kuma su zauna tare da Jonatan a Gibeya ta Biliyaminu, sauran jama'a kuwa ya sallame su, su koma gida, kowa zuwa alfarwarsa.


Magabta suna cikin Ayiyat! Sun bi ta Migron! Sun bar kayayyakinsu a Mikmash!


Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?” Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”


Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya?


Ɗaya dutsen yana wajen arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma yana daga kudu a gaban Geba.


Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.”


Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.


Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.”


Sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ni kuwa ban riga na roƙi Ubangiji ba,’ don haka ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa!”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ