Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 12:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Yanzu dai rani ne, ko ba haka ba? Zan roƙi Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama, da haka za ku sani, ku kuma ga babbar muguntar da kuka yi wa Ubangiji da kuka roƙa a yi muku sarki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 12:17
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu.


Yabo bai dace da wawa ba, kamar yadda dusar ƙanƙara ba ta dace da lokacin zafi ba, ko ruwan sama a lokacin girbi.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!


Musa da Haruna firistocinsa ne, Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne. Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.


Sa'an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra'ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce, “Ke rana, ki tsaya a Gibeyon, Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.”


Sama'ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra'ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu'a ga Ubangiji dominku.”


Amma Sama'ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji.


To, ga sarkin da kuka zaɓa nan, kuka roƙa. Ga shi, Ubangiji ya naɗa muku shi.


Suka ce wa Sama'ila, “Ka yi wa bayinka roƙo ga Ubangiji Allahnka don kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”


Kashegari, Musa ya ce wa mutane, “Kun aikata babban zunubi. Yanzu kuwa zan tafi wurin Ubangiji, watakila zan iya yin kafara domin zunubanku.”


Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga Sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama mai nasara.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ