Sa'ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da 'yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
Sa'ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa'ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa.