Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 1:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Sa'ad da ta yaye yaron, sai ta ɗauke shi, ta kuma ɗauki bijimi bana uku, da mudun gari, da salkar ruwan inabi, ta kai shi ɗakin Ubangiji a Shilo, yaron kuwa yana ɗan ƙarami.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 1:24
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


“Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi.


Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”


Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.


Ita kuwa ta haifa masa ɗa, Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a gidan Fir'auna. Genubat kuwa ya zauna tare da 'ya'yan Fir'auna, maza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ