Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 1:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Amma Hannatu ba ta tafi ba, sai ta ce wa mijinta, “Da zarar an yaye yaron, zan kai shi domin ya zauna a gidan Ubangiji muddin ransa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Hannatu kuwa ba tă bi su ba. Ta gaya wa mijinta cewa, “Sai bayan na yaye yaron, zan kai shi in miƙa shi a gaban Ubangiji, yă kuma kasance a wurin koyaushe.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 1:22
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka nake miƙa shi ga Ubangiji muddin ransa. Ya zama na Ubangiji.” A can ya yi wa Ubangiji sujada.


Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”


Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari'ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji


Yaron nan Sama'ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba.


Yaron nan Sama'ila yana ta aiki gaban Ubangiji, yana sāye da falmaran.


Sa'an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.


“Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi.


“Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


Ubangiji ya yi muhimmin alkawari, Ba kuwa zai fasa ba! “Za ka zama firist har abada Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”


Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji, Abu ɗaya kaɗai nake bukata, Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji, In yi ta al'ajabin alherinsa Dukan kwanakin raina, In roƙi biyarwarsa a can.


Hakika, alherinka da ƙaunarka Za su kasance tare da ni muddin raina. Haikalinka zai zama gidana har abada.


Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.”


to, sai ubangijinsa ya kawo shi a gaban Allah a ƙofa ko a madogarar ƙofa, sa'an nan ubangijinsa ya huda kunnensa da abin hudawa. Zai bauta wa ubangijinsa muddin ransa.


Sama'ila kuwa ya ce wa Saul, “Ka yi wauta, ba ka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba. Dā Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra'ila har abada.


Sai Dawuda ya ce, “Za ka ga abin da baranka zai yi.” Akish ya ce wa Dawuda, “Da kyau, zan sa ka cikin zaunannun jarumawan da suke kāre ni.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ