Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.
Ina rubuta wannan ne sa'ad da ba na tare da ku, domin sa'ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin!
Ni kuwa na amsa musu na ce, ba al'adar Romawa ba ce a yi wa wani hukunci, don faranta wa wani rai, ba tare da masu ƙarar, da wanda aka kai ƙara, sun kwanta a gaban shari'a ba, ya kuma sami damar kawo hanzarinsa game da ƙarar da aka tāsar.