Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 9:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Duk masu wasan gasa, sukan hori kansu ta kowane hali. Su kam, suna yin haka ne, don su sami lada mai lalacewa, mu kuwa marar lalacewa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 9:25
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mai wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ba zai sami ɗaukaka ba, sai ko ya bi dokokin wasan.


Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.


Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa'ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.


Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da kake da shi kankan, kada wani ya karɓe maka kambinka.


Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.


sanin ya kamata da kamunkai, kamunkai da jimiri, jimiri da bin Allah,


Sa'ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa.


mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama,


da tawali'u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari'a ta kama su.


Saboda haka, sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa,


Famarku da zunubi ba ta kai har yadda za a kashe ku ba.


Sa'ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa'an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa, “An shafe mutuwa da aka ci nasararta.”


sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,


Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu.


Amma yă kasance mai yi wa baƙi alheri, mai son abu nagari, natsattse, mai kirki, tsarkakakke, mai kamunkai,


Dattawa su kasance masu kamunkai, natsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ