Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 9:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Na yi wannan ne duk saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 9:23
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.


Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, saboda bishara kuma, tattalinsa ya yi.


to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu.


Don kuwa mun zama masu tarayya da Almasihu, muddin muna tsaye da ƙarfi a kan amincewar nan tamu ta fari, har zuwa ƙarshe.


Amma ko kaɗan ba mu sakar musu ba, ko da taƙi, domin gaskiyar bishara tă zaune muku.


Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,


Ma'aikaci, ai, shi ya kamata yă fara cin amfanin gonar.


Na rubuto muku ne ina a cikin wahala da baƙin ciki gaya, har da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin ku san irin tsananin ƙaunar da nake yi muku.


Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba? Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa.


Don haka, ku dattawan ikkilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikkilisiya, ɗan'uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi,


Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni'imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,


Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu.


Ashe, ba ku sani ba, a wajen tsere dukan masu gudu suna ƙoƙarin tsere wa juna, amma ɗaya ne kaɗai yake samun kyautar ci? To, sai ku yi ta gudu haka nan, don ku ci.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ