Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 8:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Amma in wani mutum, wanda yake da rarraunan lamiri, ya gan ka, kai da kake da sani, kana ci a ɗakin gunki, ashe, wannan ba zai ƙarfafa lamirinsa har ya ci abincin da aka miƙa wa gunki ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 8:10
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun sani, duk duniyar nan gunki yana a matsayin abin da babu ne, da kuma, babu wani Allah sai ɗaya.


Wanda yake shakka, amma kuwa ya ci, ya sani ya yi laifi ke nan, domin ba da bangaskiya ya ci ba. Duk abin da ba na bangaskiya ba ne, zunubi ne.


Amma dai ba kowa ne yake da wannan sani ba. Amma waɗansu ta wurin sabawarsu da al'amuran gunki har yanzu, sukan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda haka lamirinsu, da yake rarrauna ne, ya ƙazantu.


Na sani, na kuma tabbata, a tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne yake marar tsarki.


A duk wuraren sujadarsu sukan kwanta A bisa tufafin da suka karɓe jingina. A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sha ruwan inabi Da suka karɓo daga wurin waɗanda suke bi bashi.


Suka tafi gona, suka ɗebo inabi, suka matse, suka yi biki a gidan gunkinsu. Suka ci, suka sha, suka zazzagi Abimelek.


Waɗannan mata sukan gayyaci mutanen zuwa wajen shagalin tsafinsu. Isra'ilawa kuwa sukan ci abinci, su kuma yi sujada ga gumaka.


Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al'ummai ko ikkilisiyar Allah,


sai dai mu rubuta musu wasiƙa, su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.


Sai dai ku lura, kada 'yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ