20 Kowa yă zauna a maƙamin da Allah ya kiraye shi.
20 Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi.
Sai dai kowa yă yi zaman da Ubangiji ya sa masa, wanda kuma Allah ya kira shi a kai. Haka nake umarni a dukan Ikilisiyoyi.
kuna himmantuwa ga zaman lafiya, kuna kula da sha'anin gabanku kawai, kuna kuma aiki da hannunku, kamar yadda muka umarce ku,
To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki da natsuwa, suna ci da kansu.
Mutumin da ya bar gida yana kama da tsuntsun da ya bar sheƙarsa.
In da igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi tsinkewa. In kuwa ba igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi aure.