Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 7:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Amma don gudun fasikanci sai kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 7:2
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta haka ya wajaba maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan suke yi wa. Ai, wanda ya ƙaunaci matarsa, ya ƙaunaci kansa ke nan.


Duk da haka dai, sai kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta yi wa mijinta ladabi.


In kuwa ba za su iya kamewa ba, to, sai su yi aure. Ai, gwamma dai a yi aure da sha'awa ta ci rai.


Idan ka sami mace ka sami abu mai kyau, wannan alheri ne wanda Ubangiji ya yi maka.


Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.


Su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.


Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka.


Mutum na iya cin gādon gida da kuɗi daga wurin iyayensa, amma Ubangiji ne kaɗai yake ba shi mace mai hankali.


Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”


To, a yanzu, a game da abin da kuka rubuto, yana da kyau mutum ya zauna ba aure.


Miji yă ba matarsa hakkinta na aure, haka kuma matar ga mijinta.


kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,


Sa'ad da iyayensu ko 'yan'uwansu sun kawo ƙara gare mu, za mu ce musu, ‘Ku bar mana su, muna roƙonku, domin ba daga wurin yaƙi muka kamo su domin su zama matanmu ba. Amma tun da ba ku ba mu su ba, ba ku da laifin ta da alkawari.’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ