Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.
Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.
Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.
Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.
Almasihu ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak, ba ƙari, ba kuwa ta wurin jinin awaki ko na 'yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta wurin nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa.
Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”
Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa, “Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa, Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma,
Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.
Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.