1 Korintiyawa 6:2 - Littafi Mai Tsarki2 Ashe, ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari'a? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari'a, ashe, ba za ku iya shari'ar ƙananan al'amura ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.