Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 5:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita, da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 5:10
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

In wani a cikin marasa ba da gaskiya ya kira ku cin abinci, kuka kuwa yarda ku tafi, sai ku ci duk irin da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.


Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.


Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.


Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu.


don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,


waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al'amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu.


Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.


To, ina masu hikima suke? Ina kuma masana? Ina masu muhawwarar zamanin nan? Ashe, Allah bai fallashi hikimar duniyar nan a kan wauta ce ba?


Sai ya ce musu, “Ku daga ƙasa kuke, ni kuwa daga sama nake. Ku na duniyan nan ne, ni kuwa ba na duniyar nan ba ne.


Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.


Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙa wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne.


“Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka.


Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.


Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.


Na rubuta muku a cikin wasiƙata, cewa kada ku yi cuɗanya da fasikai.


Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ