1 Korintiyawa 4:7 - Littafi Mai Tsarki7 Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.