Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 4:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Domin Mulkin Allah ba ga maganar baka yake ba, sai dai ga ƙarfi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 4:20
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu,


domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana,


Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa'an nan kuma al'ummai.


ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.


amma ga waɗanda suke kirayayyu, ko Yahudawa ko al'ummai duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, da hikimar Allah.


Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba zan kunyata ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ