18 Waɗansu har suna ɗaga kai, kamar ba zan zo wurinku ba.
18 Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai.
A! Har kuwa alfarma kuke yi! Ashe, ba gwamma ku yi baƙin ciki ba, har a fitar da wanda ya yi wannan mugun aiki daga cikin jama'arku?
To, me kuka zaɓa, in zo muku da sanda, ko kuwa da fuskar ƙauna da lumana?
ina roƙonku kada ku tilasta ni in matsa muku sa'ad da na zo, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha'anin duniya ne.
Ina tsoro kada watakila in na zo in same ku ba a yadda nake so ba, ku kuma ku gan ni ba a yadda kuke so ba, ko ma a tarar da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da yanke, da tsegunguma, da girmankai, da tashin hankali.