Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 2:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 2:4
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin Mulkin Allah ba ga maganar baka yake ba, sai dai ga ƙarfi.


domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana,


Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.


Sa'ad da na zo wurinku, 'yan'uwa, ban zo ina sanar da ku asiran Allah ta wurin iya magana ko gwada hikima ba.


ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.


Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa'ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran.


Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al'amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.


Na faɗi wannan ne don kada kowa ya hilace ku da maganar yaudara.


Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,


An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.


To, wato ni son mutane nake nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya? Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.


Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai.


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


Suna faɗar ƙarya, suna kuma yin duban ƙarya, suna cewa, ‘Ubangiji ya ce,’ alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba, duk da haka sun sa zuciya ga cikawar maganarsu.


Ta jarabce shi da kwarkwasarta, sai ya ba da kai ga daɗin bakinta.


Sai Agaribas ya ce wa Bulus, “Wato a ɗan wannan taƙaitaccen lokaci kake nufin mai da ni Kirista?”


Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”


A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki ya gaya mana amsar ka-cici-ka-cicin, idan kuwa kin ƙi, to, za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Kun gayyace mu don ku tsiyata mu ne?”


Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’


Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.


Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.


Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka, da sani, da haƙuri, da kirki, da Ruhu Mai Tsarki, da sahihiyar ƙauna,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ