Ko da yake an gicciye shi ne da rashin ƙarfi, duk da haka a raye yake ta ikon Allah. Mu ma marasa ƙarfi ne kamarsa, amma a game da al'amuranku da za mu zartar, a raye muke tare da shi, ta ikon Allah.
Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,
Ko a lokacin da muka zo ƙasar Makidoniya ma, ba mu sami shaƙatawa ba, ana ta wahalshe mu ta kowace hanya, a waje ga husuma, a zukatanmu kuma ga fargaba.
Lokaci zai yi in da zuciyar mutanen Masar za ta narke kamar mata. Za su yi rawar jiki da razana lokacin da suka ga Ubangiji Mai Runduna ya miƙa hannunsa don ya hukunta su.
Ransa kuma yana a gare ku fiye da dā ƙwarai, duk sa'ad da yake tunawa da biyayyarku, ku duka, da kuma yadda kuka yi na'am da shi a cikin halin bangirma tare da matsananciyar kula.