4 In ya kyautu ni ma in tafi, to, sai su raka ni.
4 In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.
ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikilisiyoyi sun zaɓe shi ya riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.
Sun roƙe mu ƙwarai da gaske mu yi musu alheri su ma, a sa su a cikin masu yi wa tsarkaka gudunmawa,
Amma a yanzu kam, za ni Urushalima, don in kai wa tsarkaka gudunmawa.
Sa'ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai taimakonku Urushalima.
Zan zo gare ku bayan na zazzaga ƙasar Makidoniya, don kuwa ta Makidoniya zan bi.