Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 16:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la'ananne. Ubangijinmu fa yana zuwa!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 16:22
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.


Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.”


Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.


Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu.


Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni.


Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.


Shi wanda ya shaida abubuwan nan ya ce, “Hakika, ina zuwa da wuri.” Amin! Zo, ya Ubangiji Yesu.


A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to, “Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”


Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Da ma a la'ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, 'yan'uwana na kabila!


In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.


Don haka nake sanar da ku, cewa ba mai magana ta wurin ikon Ruhun Allah sa'an nan ya ce, “Yesu la'ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.


Sai suka je wurin manyan firistoci da shugabanni, suka ce, “Mun yi wata babbar rantsuwa, cewa za mu zauna ba ci ba sha sai mun kashe Bulus.


Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.


Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.


“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina.


Ku saurara in raira muku wannan waƙa, Waƙar abokina da gonar inabinsa. Abokina yana da gonar inabi A wani tudu mai dausayi.


Bakinsa yana da daɗin sumbata, Kome nasa yana faranta mini rai. Matan Urushalima, yadda ƙaunataccena yake ke nan.


Faɗa mini, ƙaunataccena, Ina za ka kai garkenka kiwo? Ina za su huta sa'ad da rana ta take? Ina zan neme ka a cikin garkunan makiyaya?


Bari kowa ya san jimirinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ