Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.
Amma ga shi, a yanzu da Timoti ya dawo daga wurinku, ya yi mana albishir a kan bangaskiyarku da ƙaunarku, da kuma yadda kuke tunawa da mu da alheri a koyaushe, har kuna begen ganinmu, kamar yadda mu ma muke yi.