Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,
Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka ta da Almasihu daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.
Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”
tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari'a, shari'a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”
Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah.
domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa'ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.”
Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa'ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye.
Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu.