Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”
domin Ubangiji kansa ma zai sauko daga Sama, da kira mai ƙarfi, da muryar babban mala'ika, da kuma busar ƙahon Allah. Waɗanda suka mutu suna na Almasihu, su ne za fara tashi,
Muna kuwa shaida muku bisa ga faɗar Ubangiji, cewa mu da muka wanzu, muke kuma a raye har ya zuwa komowar Ubangiji ko kaɗan ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba,