Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 15:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A yanzu kuma, 'yan'uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 15:1
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi.


har kuka zama masu koyi da mu, da kuma Ubangiji, kuka kuma karɓi Maganar Allah game da farin cikin da Ruhu Mai Tsarki yake sawa, ko da yake ta jawo muku tsananin wahala.


Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a'a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.


To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu.


Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,


Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.


A wannan rana Allah zai yi wa 'yan adam shari'a a kan asiransu, ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga bishara da nake wa'azinta.


To, manzanni da 'yan'uwan da suke a ƙasar Yahudiya suka ji, cewa al'ummai ma sun yi na'am da Maganar Allah.


Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe.


Ni na yi shuka, Afolos ya yi banruwa, amma Allah ne ya girmar.


Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah.


Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.


Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah.


Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara.


Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ