Sa'ad da kuka tafi yaƙi a ƙasarku gāba da maƙiyanku da suke matsa muku lamba, sai ku yi busar faɗakarwan nan da kakakin, Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, ya cece ku daga maƙiyanku.
Ku busa ƙaho, ku yi gangami, A cikin Sihiyona, tsattsarkan dutsen Allah! Duk mutanen ƙasar za su yi rawar jiki, Domin ranar Ubangiji tana zuwa, ta yi kusa.
A wannan rana za a busa ƙaho don a kirawo Isra'ilawan da suke zaman baƙunci a Assuriya da Masar. Za su zo su yi wa Ubangiji sujada a Urushalima a tsattsarkan dutsensa.