Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 14:16 - Littafi Mai Tsarki

16 In ba haka ba, in ka gode wa Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake jahili zai ce, “Amin,” a kan godiyar da kake yi, in bai san abin da kake faɗa ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 14:16
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai rayayyun halittan nan huɗu suka ce, “Amin! Amin!” Dattawan nan kuma suka fāɗi suka yi sujada.


Sai mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila, Mu yabe shi yanzu da har abada kuma! Dukan jama'a za su amsa su ce, “Amin! Amin!” Ku yabi Ubangiji!


Ku yabi Ubangiji Allah na Isra'ila! Ku yi ta yabonsa har abada abadin! Sa'an nan dukan jama'a suka ce, “Amin, Amin,” suka yabi Ubangiji.


bayan da ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya gutsuttsura, ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake saboda ku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.”


“Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka, Ubangiji ya sa annabcin da ka yi ya zama gaskiya, Ubangiji ya komo da kayayyakin Haikalinsa da dukan waɗanda aka kai su zaman talala a Babila.


Sai Ezra ya yabi Ubangiji Allah Maɗaukaki. Jama'a duka suka amsa, “Amin, amin!” suna ɗaga hannuwansu. Suka sunkuyar da kansu har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada.


suna cewa, “Hakika! Yabo, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da girma, da iko, da ƙarfi su tabbata ga Allahnmu har abada abadin! Amin! Amin!”


Bari ruwan nan ya shiga cikinki, ya sa cikinki ya kumbure, cinyarki kuma ta shanye.” Sai matar ta amsa, ta ce, “Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka.”


Shi wanda ya shaida abubuwan nan ya ce, “Hakika, ina zuwa da wuri.” Amin! Zo, ya Ubangiji Yesu.


Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙauna, albarkar Almasihu Yesu.


In na yi addu'a da wani harshe, ruhuna ne yake addu'a, amma tunanina bai amfana kowa ba.


Duk wanda yake magana da wani harshe, ba da mutane yake magana ba, da Allah yake yi, ba kuwa wanda yake fahimtarsa, domin asirtattun al'amura yake ambato ta wurin Ruhu.


To, da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yahaya, suka kuma gane marasa ilimi ne, talakawa kuma, suka yi mamaki, suka kuwa shaida su, a kan dā suna tare da Yesu.


Akwai waɗansu al'amura kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta kowannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.


Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan yake da karatu haka, ga shi kuwa, bai taɓa koyo ba?”


Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’


Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ” Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”


Ku yabi sunansa mai daraja har abada, Allah ya sa ɗaukakarsa ta cika dukan duniya! Amin! Amin!


Bari mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila. Ku yabe shi yanzu da har abada! Amin! Amin!


Sai kuma na kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, ya wofintar da shi.” Sai dukan taron suka amsa, “Amin, amin.” Suka kuma yabi Ubangiji. Suka kuwa cika alkawarin da suka yi.


Sai Benaiya ɗan Yehoyada ya ce wa sarki, “Za a yi haka, Ubangiji Allah na ubangijina, sarki, ya tabbatar da haka.


Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a.


Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi take, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ