Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.
Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa, “Abubuwan da ido bai taɓa gani ba, Kunne bai taɓa ji ba, Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba, Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”
Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko? Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa? Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa? Wa kuma ya kafa iyakar duniya? Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa? Hakika ka sani!
Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.