Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari'ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.
Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.
Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’