Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.
Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.
Sa'ad da nake yaro, nakan yi magana irin ta ƙuruciya, nakan yi tunani irin na ƙuruciya, nakan ba da hujjojina irin na ƙuruciya. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin ƙuruciya.
Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a'a. sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi.