Duk da haka dai a taron ikkilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar a game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.
To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikkilisiya.