A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri.
sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.