20 Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya.
20 Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya.
Jiki ba gaba ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa.
Wato, kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu.
haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan'uwansa ne.
Da dukan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin?
Ba dama ido yă ce wa hannu, “Ba ruwana da kai,” ko kuwa kai yă ce wa ƙafafu, “Ba ruwana da ku.”