Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 12:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Wato, kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 12:12
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.


To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.


bai kuwa manne wa kan ba, wanda ta gare shi ne dukkan jiki yake amfana, yake kuma a haɗe, ta wurin gaɓoɓi da jijiyoyi, yake kuma girma da girman da Allah yake sawa.


Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan.


Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci.


Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici.


Don miji shi ne shugaban matarsa, kamar yadda Almasihu yake shugaban Ikkilisiya, wato, jikinsa, shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin.


domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar Ikkilisiya, domin a inganta jikin Almasihu,


To, alkawaran nan, an yi wa Ibrahim ne, da kuma wani a zuriyarsa. Ba a ce, “Da zuriya” ba, kamar suna da yawa. A'a, sai dai ɗaya kawai, aka ce, “Wani a zuriyarka,” wato Almasihu.


To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,


Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.


An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu, don kyautata wa duka.


Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ