31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za a hukunta mu ba.
31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba.
In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.
Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.
Sai dai kowa ya auna kansa, sa'an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon.
Shi ya sa da yawa daga cikinku suke da rashin lafiya da rashin ƙarfi, har ma waɗansu da dama suka yi barci.
In kuwa Ubangiji ne yake hukunta mu, to, muna horuwa ke nan, don kada a yanke mana hukunci tare da sauran duniya.