Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 11:22 - Littafi Mai Tsarki

22 A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina Ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da kome? To, me zan ce muku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A'a, ba zan yaba muku ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 11:22
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.


Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al'ummai ko ikkilisiyar Allah,


don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.


Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikkilisiyar Allah?


A game da umarnin nan kuwa, ban yaba muku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin kirki ce.


Ina yaba muku ne don kuna tunawa da ni a cikin kowace harka, kuna kuma riƙe ka'idodin nan da kyau, daidai yadda na ba ku.


Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikkilisiyar Allah.


In kuwa wani yana jin yunwa, sai yă ci a gida, kada yă zamana taronku ya jawo muku hukunci. Batun sauran abubuwa kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ