Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.
Suna jin daɗin miƙa hadayu don cin naman, Amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Ubangiji zai tuna da muguntarsu, Zai hukunta su saboda zunubansu. Za su koma Masar.
suna shan sakamakon muguntarsu. Sun ɗauka a kan jin daɗi ne a yi annashuwa da rana kata. Sun baƙanta, sun zama abin kunya. Sun dulmuya ga ciye-ciye da shaye-shaye, suna ta nishaɗi a cikinku.