Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 10:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al'ummai ko ikkilisiyar Allah,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 10:32
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

kamar dai yadda nake ƙoƙarin kyautata wa dukan mutane a cikin duk abin da nake yi, ba nema wa kaina amfani nake yi ba, sai dai in amfani mutane da yawa, don su sami ceto.


Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu yă zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan'uwansa,


Ba ma zamar wa kowa sanadin tuntuɓe, don kada a aibata aikinmu,


Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan'uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa ɗan'uwana tuntuɓe.


Saboda haka, a kullum nake himma in kasance da lamiri marar abin zargi a wurin Allah da wurin mutane.


don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.


A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina Ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da kome? To, me zan ce muku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A'a, ba zan yaba muku ba.


Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikkilisiyar Allah?


domin ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu,


zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.


Sai dai kowa yă yi zaman da Ubangiji ya sa masa, wanda kuma Allah ya kira shi a kai. Haka nake umarni a dukan Ikilisiyoyi.


A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri.


Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikkilisiyar Allah.


Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, tare da dukan tsarkaka na duk ƙasar Akaya.


Kun dai ji irin zamana na dā a cikin addinin yahudanci, yadda na riƙa tsananta wa Ikkilisiyar Allah ƙwarai da gaske, har ina ta watsa ta,


a wajen himma kuwa mai tsananta wa Ikkilisiya ne ni, wajen aikin adalci kuwa bisa ga tafarkin Shari'a, marar abin zargi nake.


'Yan'uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da suke na Almasihu Yesu, waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,


Sai ta kwanta a wajen ƙafafunsa har safiya. Sa'an nan ta tashi tun da jijjifi kafin a iya gane fuskar mutum, gama ba ya so a sani mace ta zo masussukar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ