Ya koya muku tawali'u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.
Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa, Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi, Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.
Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ga shi, zan sauko muku da abinci daga sama. A kowace rana jama'a za su fita su tattara abin da zai ishe su a yini, da haka zan gwada su, ko za su kiyaye maganata, ko babu.
Sa'ad da Isra'ilawa suka gan shi, suka ce wa junansu, “Manna,” wato “Mece ce wannan?” Gama ba su san irinta ba. Musa kuwa ya ce musu, “Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci.