kamar dai yadda nake ƙoƙarin kyautata wa dukan mutane a cikin duk abin da nake yi, ba nema wa kaina amfani nake yi ba, sai dai in amfani mutane da yawa, don su sami ceto.
Ga shi, na yi shirin zuwa wurinku, zuwa na uku, ba kuwa zan nauyaya muku ba, don ba abinku nake nema ba, ku nake nema, domin ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran.