Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 10:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 10:17
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan'uwansa ne.


Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.


To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.


Wato, kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu.


Saboda haka, sai ku watsar da ƙarya, kowa yă riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne.


Domin ta gare shi ne dukkan jiki yake a game, yake kuma a haɗe, ta wurin gudunmawar kowace gaɓa, ta wurin kuma aikin kowace gaɓa daidai jikin yake ƙara girma, yana kuma ingantuwa da halin ƙauna.


Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan.


A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.


wato, yadda ta wurin bishara al'ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.


bai kuwa manne wa kan ba, wanda ta gare shi ne dukkan jiki yake amfana, yake kuma a haɗe, ta wurin gaɓoɓi da jijiyoyi, yake kuma girma da girman da Allah yake sawa.


Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ