Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”
Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.
Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.
Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.
Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal'amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra'ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.
Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.
Ashe, tun dā tsammani kuke yi muna kawo hanzarinmu a gare ku ne? A'a, a gaban Allah muke magana, muna na Almasihu, wannan kuwa duk domin inganta ku ne, ya ku ƙaunatattu.
Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.