Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,
Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.
ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.
Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.
wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.
Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?
Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.
Da daddare sai Ubangiji ya tsaya a kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.”
Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida, domin ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa.
Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.