Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Bitrus 5:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Kada ku nuna wa waɗanda suke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Bitrus 5:3
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba don ba mu da halaliya a wurinku ba ne, a'a, sai dai don mu zama abin misali a gare ku kawai, don ku yi koyi da mu.


Ya ku 'yan'uwa, ku yi koyi da ni dukanku baki ɗaya, ku kuma dubi waɗanda zamansu yake daidai da gurbin da muka bar muku.


Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.


Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a'a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.


Kai ma sai ka zama gurbi na aiki nagari ta kowace hanya, da koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da natsuwa,


Kada ka yarda kowa yă raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka.


Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


Abin da kuka koya, kuka yi na'am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah mai zartar da salama zai kasance tare da ku.


Domin ba wa'azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.


Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.


Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā.


Ka tuna da jama'arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni, Ka tuna da jama'arka waɗanda ka fansa, Don su zama kabilarka. Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!


Mai farin ciki ce al'ummar da Ubangiji yake Allahnta, Masu farin ciki ne jama'ar da Ubangiji ya zaɓo wa kansa!


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa, Yakubu shi ne rabon gādonsa.


gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.


To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?


Da kai, da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”


Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku


Ku ma har kuka zama abin koyi ga dukan masu ba da gaskiya a ƙasar Makidoniya da ta Akaya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ