Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
Sai na ji kowace halittar da take a Sama, da ƙasa, da ƙarƙashin ƙasa, da bisa teku, da kuma dukkan abin da yake cikinsu, suna cewa, “Yabo, da girma, da ɗaukaka, da mulki sun tabbata ga wanda yake a zaune a kan kursiyin, da Ɗan Ragon nan, har abada abadin!”