Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Bitrus 3:20 - Littafi Mai Tsarki

20 wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Bitrus 3:20
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.”


Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.


Sai Nuhu ya fito, da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa tare da shi,


Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.


Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”


A wannan rana Nuhu da 'ya'yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan 'ya'yansa tare suka shiga jirgin,


Ku ɗauki haƙurin Ubangijinmu, ceto ne. Haka ma, ƙaunataccen ɗan'uwanmu Bulus ya rubuto muku, bisa ga hikimar da aka ba shi,


To, ƙaƙa fa? Allah da yake yana so ya nuna fushinsa, ya kuma bayyana ikonsa, sai ya haƙura matuƙar haƙuri da waɗanda suka cancanci fushinsa, suka kuma isa hallaka,


“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.


Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.


Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye.


domin ya miƙa ta ga Allah, tsarkakakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin Kalma,


Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.


Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.


kuna samun ceton rayukanku, ta wurin sakamakon bangaskiyarku.


Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.


A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.


Da ruhun ne kuma ya je ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku shela,


Saboda haka, sai duk masu shan wuya bisa ga nufin Allah su danƙa ransu ga Mahalicci mai aminci suna aikata abin da yake daidai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ