Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.
Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa,
Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.
Kada ka yarda kowa yă raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka.
Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,